Wasanni - Yadda NFF ta ki karrama Isma'ila Mabo (2)

Share:

Listens: 0

Wasanni

Miscellaneous


Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya dora ne kan na makon jiya, inda yake tattaunawa kan rashin gayyatar tsohon kocin tawagar mata ta Najeriya Super Falcon, Isma'ila Mabo zuwa bikin karramar tsoffin 'yan wasan mata da ya horas har suka kafa gagarumin tarihi a Najeriya. Wani abu da ya zafafa cece-kuce kan lamarin shi ne yadda aka gayyato hatta matan da ke zaune a Amurka da Turai amma aka mance da Mabo wanda ke zaune a garin Jos na jihar Filato.