News
A yau shirin batun Noma da kiwo zai waiwaya a Najeriya, ganin yadda har yanzu aka gaza samun matsaya guda tsakanin gwamnatin kasar a matakin tarayya da kuma gwamnonin jihohi musamman na yankin Kudanci, kan yadda za a bullowa matsalar rikicin manoma da makiyaya da sauran batutuwa masu alaka da matsalar ciki har da neman kawo karshen tsarin kiwon gargajiya na yawon da makiyaya a Najeriyar ke yi a tsakanin yankunan arewaci da kudancin kasar.

