News
Shirin 'Kasuwa akai miki Dole' na wannan mako ya maida hankali ne dangane da shirin gwamnatin Najeriya na tallafawa manoma da kuma kananan sana’o’i. Shirin wanda Babban Bankin Najeriya CBN ya kirkirir karamin bankin tsimi da tanadi na musamman da akayi wa suna da NIRSAL dake tallafawa manoma da kananan ‘yan kasuwa basuka maras kudin ruwa cikin sauki, batare da jingina ba, kamar yadda aka saba a wasu bankunan kasuwanci. To sai dai kuma duk da wadan nan tanade-tanade da shugaban bankin ya zayyana, wasu shugabannin kungiyoyin manoma da dai-daikon ‘yan kasuwa da akayi tanadin dominsu na kokawa dangane da tafiyar hawainiya da suka ce Shirin keyi. Haka zalika, akwai dai zarge-zarge da dama kan wannan shiri, kama daga zargin sai mai uwa a gidin murhu ke samun wannan tallafi, da kuma batun karban na garo daga ma’aikatan wannan baki, sai kuma uwa uba, akwai majiyoyin da suka tabbatar da ware kaso mai tsoka ga gwamnonin Najeriya, wato kalilan daka cikin ‘yan Najeriya yaku bayu da akayiwa tanadi ke moran wannan shiri.