News
Shirin 'Kasuwa a kai miki Dole' na wannan mako ya maida hankali ne kan wani gagarumin taro da kungiyar Masu Masana’antu ta Najeriya MAN ta shirya a birnin Lagos dake Kudancin kasar, yayin da take bukin cikar ta shekaru 50 da kafuwa. Kungiyar Masu Masa’antun Najeriya karkashin jagorancin Injiniya Mansur Ahmed ta shirya taron ne a katsaitacen otel din Intercontinental dake birnin Lagos, inda ta shirya muhawara mai matukar muhimmaci kan bunkasar Masana’antu da kuma ci gaba mai daurewa. Taken wannan taro dai shine, yadda”Masana'antu zasu zama Hanyoyin Cimma Manufofin Ci Gaba mai Dorewa" kamar yadda wani kudiri na Majalisar Dinkin Duniya ya tanadar, don haka aka gayyaci ƙwararru a fannin masana'antu da kuma masu ruwa da tsaki a sabgar, ciki harda Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Hajiya Amina Mohammed wanda ta halarci taron na Lagos kai staye ta fasahar Bidiyo, kuma ta yi tsokaci kamar haka.